A dai dai lokacinda hukumomin kasar Bahrai suka bada sanarwan fara sauran karar da suka shigar a kan Aya. Isa Kasim shugbannyan shi'ar kasar Bahrai a jiya magoya bayansa sun fito kan titunan kasar da kumaji don nuna rashin amincewarsu da hakan.
A ranar 26 ga watan Yulin da muke ciki ne wata kotu a kasar Bahrain ta fara sauraron tuhumce tuhumce wadanda sarakunan Ali Khalifa na kasar Baharai suka shigar kan Shiek Isa Kasim, shugaban yan mazhabar shia a kasar. Dubban daruruwan magoya Aya. Sheukh Isa ne a duk fadin kasar da kuma kungiyu kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa suka fito zanga zangar yin All.. wadai da hakan.
Kafin haka dai hukumomi na kasar Bahari sun bayyana kwace yan kasancin Sheikh Isa Kasim a matsayin dan kasar ta Bahrain. Kuma tun lokacin ne dai dubban daruruwan magoya bayan malamin suke zaman dirshen a kofar gidansa da ke "الدراز" a cikin kasar.
Jami'an tsron kasar ta Bahrain dai sun dauki matakan tsaro mafi tsanani don ganin zanga zangar bai watsu zuwa birnin Manama babban birnin kasar ba. Daya faga cikin tuhumar da akewa malamin dai sun hada da karban kudaden khumusi wanda wajibi ne a sharia daga hammum mutanen kasar ba tare da izinin gwamnati ba.
A nasu bangaren babbar majalisar malaman kasar Bahrai ta fidda wani bayani wanda a cikinsa suka bayyana cewa gurfanar da Sheikh Isa Kasim a gaban kuliya da wannan tuhumar kamar tashe keyyar mazhabar shi'a ne a wacce wacce take da mabiya fiye da kashi 80% na mazaunar kasar.
Har'ila yau cibiyar yada labarai ta العهد ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa kungiyoyin kare hakkin bil'adama fiye da 90 a kasashen duniya da dama sun fidda bayanai na yin All..wadai da matakan da hukumomin kasar Bahrain suke dauka a kan yan shi'a a kasar da kuma musamman kan shugabanninsu wadanda suka hada da Sheikh Isa Qasim.
A wani bangare kuma Amir Abdullahiyon wakilin shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa babu wata hanya ta warware rikicin kasar Bahrai sai ta tattaunawa da kuma siyasa. Ya kara da cewa yakamata hukumomin kasar Bahrai su dauki darasi a tahiri don, don uslubin da suke bi wajjen murshe nutanen kasar Bahrain masu neman hakkinsu a bisa dako ba zai taba haifar masu da mai ido ba.
Wakilin shugaban Majalisar ya kammala da cewa wulakanta sheikh Isa Kasam ba abinda zai karawa hukumomin Bahrain sai kara kiyayya da ga mutanen kasar da kuma kara rufe hanyar warware matsalar da ta hanyar lumana.288